Wakilan kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya sun isa Paris a kokarin da suke yi na neman sayen Neymar, daga PSG. (CBS)
A shirye Chelsea take ta bayar da Romelu Lukaku, da dan bayan Senegal Kalidou Koulibaly, ga Inter Milan domin kungiyar ta Italiya ta sayar mata da mai tsaron ragarta Andre Onana, na Kamaru. (Sun)
Sai dai kuma bayan wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai Onana ya ce yana son ci gaba da zama a kungiyar ta Italiya. (90 min)
Newcastle na gaban Tottenham a gogayyar zawarcin dan wasan tsakiya na Leicester City James Maddison, dan Ingila da aka yi wa kiyasin farashin fam miliyan 40. (Sky Sports)
Maddison ne dan wasan Leicester kadai da Newcastle ke so, wanda hakan na nufin kungiyar ba za ta nemi Harvey Barnes, na Ingila ba, amma kuma tana son dan wasan tsakiya na Manchester United Scott McTominay na Scotland. (Northern Echo)
Tottenham ta kusa cimma yarjejeniya tsakaninta da golan Brentford David Raya, na tawagar Sifaniya, wanda Manchester United ma ke so. (Fabrizio Romano daga Goal.com)
Dan wasan Crystal Palace na Ivory Coast Wilfried Zaha, na tattaunawa da Paris St-Germain don ganin ya koma can idan kwantiraginsa ya kare a bazara. (Sun)
Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya tana son kociyan AS Roma, Jose Mourinho, ya koma wajenta amma kuma Al-Ahli ma na sonshi. (Foot Mercato)
Liverpool za ta nemi dan wasan tsakiya na Southampton da Ingila James Ward-Prowse, kasancewar ta rasa dan wasan tsakiya na Chelsea Mason Mount, wanda zai koma Manchester United. (Mirror)
Dan wasan Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani, mai shekara 24, na cikin ‘yan gaba shida da Manchester United za ta yi zawarci, amma kuma dan wasan na tawagar Faransa yana son samun tabbaci cewa zai kasance daga cikin ‘yan wasan farko na Erik ten Hag. (Manchester Evening News)
Tuni Liverpool ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Nice Khephren Thuram, mai shekara 22, dan kasar Faransa tare da takwaransa dan Faransar shi ma Manu Kone na kungiyar Borussia Monchengladbach, mai shekara 22. (Football Insider)
Zuwa yanzu ana ganin ciniki ya riga ya fada tsakanin Arsenal da West Ham a kan Declan Rice. (Ran)
Tsohon kociyan Rangers da Aston Villa Steven Gerrard, yana duba yuwuwar karbar aikin horad da kungiyar Al-Ettifaq, ta Saudiyya, wadda take sha’awarsa sosai. (Reuters)
Arsenal ta fara tattaunawa domin sayen dan bayan Leicester Timothy Castagne, dan Belgium mai shekara 27, daga kungiyar da ta fadi daga Premier. (Goal)
Dan bayan da Tottenham ke son saye Roger Ibanez, zai bar Roma, inda kungiyar ta Italiya ke son sayar da dan Brazil din da wuri. (La Gazzetta dello Sport, ta hanyar Express)
Tsohon dan bayan Wolves Romain Saiss yana son komawa gasar Premier bayan da kyaftin din na Morocco mai shekara 33 ya bar Besiktas a bazarar da ta gabata. (Foot Mercato)
Burnley ta taya mai tsaron ragar, Anderlecht, Bart Verbruggen yuro miliyan 15. (Nieuws Blad)
Ba lalle ba ne dan bayan Atletico Madrid Renan Lodi, mai shekara 25, ya koma Nottingham Forest bayan da ya yi zaman aro a kakar da ta wuce, inda a yanzu dan Brazil din yake son tafiya kungiyar da za ta buga gasar Zakarun Turai. (Football Transfers)